Jiga-jigan APC a Kano sun yi wa Ganduje bara’a
A daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke shirin gudanar da zaɓen shugabaninta a matakin jiha, bisa ga dukkan alamu wata babbar ɓaraka ta kunno kai tsakanin manyan ƴaƴan jam’iyyar a jihar Kano.
Ɓarakar na da nasaba da zargin da jiga-jigan jam’iyyar suke yi wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere tare da yin gaban kansa wajen yanke hukunci a kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar.
A ranar Talata da daddare, wasu ƙusoshin jam’iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha’aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam’iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.
Ɗaya daga cikin jagororin APC a Kano wanda yake cikin taron da aka yi a ranar Talata ya shaida wa BBC cewa sun yanke shawarar ganawa da shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni domin bayyana masa korafe-korafensu kafin lokacin ya ƙure.
Bayanai sun nuna cewa a yammacin Laraba ne za a gudanar da taron tsakanin ƙusoshin APC na Kano da shugaban na riƙo.