Jamus Ta Ware Ranar 28 Ga Mayu Ranar Tsaftar Masu Jinin Al’ada

An ware ranar ce don karfafa muhimmanci kula da tsaftar jiki a lokacin da mace ke al’ada da kuma wayar da kan jama’a.

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Jamus da ake kira Wash United ce ta ware ranar 28 ga watan Mayu na kowace shekara a matsayin ranar tsaftar mata masu jinin al’ada, wato International Day For Menstrual Hygiene wadda ta samu karbuwa a duk fadin duniya.

An ware ranar ce don karfafa muhimmanci kula da tsaftar jiki a lokacin da mace ke al’ada da kuma wayar da kan jama’a game da irin matsalolin da matan da basa samun auduga (pad) a lokacin suke shiga.

Sa’an nan an kuma yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu, da masu ruwa da tsaki da ma sauran jama’a da su tattauna game da irin kalubalen da mata ke fuskanta a shekarun da suka isa yin al’ada.

Taken ranar na wannan shekarar shine ‘Jinin Al’ada ba abin kyama bane’.