Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce “babu wani wuri mai tsaro a Gaza”
Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana samun karancin abin da kungiyar za ta iya yi domin kare ‘yan Gazan da ke kokarin fakewa daga fadan
Thomas White, na hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce “Bari mu fayyace sosai, babu wani wuri da ke da tsaro a Gaza a yanzu.”
Jiya Juma’a PM Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ba za a tsagaita bude wuta na wucin gadi da Hamas a Gaza ba har sai an sako dukkan ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su.
Isra’ila ta kai hari kan wata motar daukar marasa lafiya a Gaza da ta ce jami’an Hamas na amfani da su
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce Isra’ila ta kai hari kan ayarin motocin daukar marasa lafiya a wurare daban-daban guda biyu, ciki har da wajen asibitin Al-Shifa.
Isra’ila ta fara kai hare-hare a Gaza bayan da Hamas ta kashe fiye da mutane 1,400 a Isra’ila tare da yin garkuwa da wasu fiye da 200.
Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutane 9,000 aka kashe a yankin tun ranar 7 ga Oktoba.