Jami’an tsaro sun kwashe Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna cikin dare
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa gamayyar jami’an tsaro sun kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.
Shugaban makarantun Dahiru Bauchi na Kaduna da kewaye kuma limamin masallacin bye pass na Kaduna, Fatahu Umar Pandogari, ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamarin.
“Da misalin 12:00 na dare Sojoji da Ƴan sanda da Kastelea da Road Safety suka shigo gidan Maulanmu Shehu, nan makaranta, suka kama almajirai suka tafi da su cikin daren,” in ji shugaban makarantar.
Ya bayyana cewa bai san dalilin da ya sa aka kama almajiran ba, amma tun bayan rufe makarantu lokacin ɓullar korona a karon farko, tun lokacin aka sallami ɗaliban makarantar, amma a cewarsa, waɗanda aka kama a yanzu waɗanda suke zaune a gidan Sheikh Dahiru ne ba wai waɗanda suka taso suka zo daga wani gari ba.
Ya kuma bayyana mana cewa sun yi ƙoƙarin tuntuɓar gwamnatin Kaduna a lokacin da abin ya faru, amma ba su samu damar magana da su ba.
Amma ko da BBC ta tuntuɓi gwamnatin Kaduna, ta shaida mana cewa a halin yanzu ba za su ce komai kan wannan lamari ba, amma nan gaba kaɗan za su fito su yi ƙarin bayani.
Babu wani tabbaci dai kan dalilin da ya sa aka kai wannan samamen, amma ko a kwanakin baya sai da gwamnatin jihar ta ƙwace lasisin wata makaranta da kuma rufe ta sakamakon zarginta da saɓa dokokin korona.
Ko a bara sai da gwamnatin jihar ta mayar da wasu almajirai garuruwansu, inda ta zarge su da yaɗa korona.
A lokacin, har sai da wannan lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin Kaduna da Kano inda Kaduna ke zargin almajiran da ake kai wa jihar da Kano ke kai korona jihar.
Hakan ya biyo bayan wasu almajirai 65 da aka kai su Kaduna daga Kano gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar korona.