ISWAP ta yi awon gaba da jami’an agaji uku

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar da’awar kafa daular Islama a yankin yammacin Afirka, ISWAP, ta yi garkuwa da wasu jami’an tsaro biyu da wasu ma’aikatan jin kai guda uku na kungiyar lafiya ta Family Health International, FHI 360 a jihar Borno.

FHI 360 ci gaban ɗan adam ce mai zaman kanta a Amurka kuma ƙungiya ce mai zaman kanta, mai sadaukar da kai don inganta lafiya da jin daɗin jama’a.

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan na ISWAP sun kai farmaki gidan baki na kungiyar masu zaman kan su a ranar Larabar da ta gabata a wani samame da suka yi da misalin karfe 4 na safe tare da lallasa wadanda abin ya shafa.

A cewar Zagazola Makama, wata mujallar yaki da tada kayar bayan da ke mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da kungiyar ta fitar tun bayan da wannan labarin ya fito.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai, OCHA, ya bayyana a cikin 2022 cewa ma’aikatan agaji da yawa ko dai sun mutu, sun jikkata ko kuma aka yi garkuwa da su a Arewa maso Gabashin Najeriya.