Isra’ila za ta binciki ‘yan sandan ta kan leƙen asiri a wayoyin mutane

Gwamnatin Isra’ila ta sanar da kafa wani kwamitin bincike kan cewa ‘yan sanda na amfani da wata manhajar leƙen asiri ga tsoffin masu taimaka wa tsohon firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu da sauran manyan ma’aikata. 

Ministan tsaron cikin gida Omer Barlev ya ce kwamitin zai binciki zarge-zargen da wata jaridar ƙasar ta rubuta mai suna Calcist (kalsayit). 

Jaridar ta rawaito cewa ‘yan sandan sun yi amfani da manhajar kutse wajen tattara bayanan sirri da suke tona asirin ministoci da magadan gari da ‘yan jarida da ma makusantan firaministan. 

Ta ƙara da cewa suna yin hakan ne ba tare da doka ta amince ba.