Idan Ba Mu Yi Da Gaske Ba, Mayakan ISWAP Za Su Fitini Najeriya – Zulum

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya da ke kula da sha’anin sojin kasar ya ziyarce shi a Maiduguri.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna “matukar” damuwa kan yadda mayakan ISWAP ke karuwa a wasu sassan jihar, lamarin da ya sa ya yi kira ga jami’an tsaro da su dauki “matakan gaggawa.”

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya da ke kula da sha’anin sojin kasar ya ziyarce shi a ranar Laraba a Maiduguri.

“Maganar gaskiya ita ce, ya zama dole mu dauki mataki akan mayakan ISWAP a jihar Borno, idan muka ki fatattakar su, ta yi wu su zama matsala ba ga yankin arewa maso gabas kadai ba, har ma da daukacin Najeriya.”

Kwamitin ya kai ziyarar ne karkashin jagorancin Sanata Mohammed Ali Ndume kamar yadda wata sanarwar da gwamnatin Bornon ta fitar ta ce.

Farfesa Zulum ya kara da cewa, “mayakan ISWAP na da makamai kuma a shirye suke sannan suna da basira fiye da mayakan Boko Haram kuma suna karuwa akai-akai, dalilin kenan da ya sa ya kamata a fatattake su.”

Gwamnan ya kuma mika godiya ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da dakarun Najeriya da masu ayyukan sa-kai saboda irin taimakon da suke bayar wa.

“Jihar Borno na ganin dawowar zaman lafiya a hankali. Hakan ya yi wu ne saboda taimako da gwamnatin tarayya ta ba mu. Sannan shugabannin jami’an tsaro su ma suna ba da nasu hadin kan. A takaice, shugabannin rundunonin soji (GOCs) su ma suna ba da nasu taimakon”.

Sai dai gwamnan ya nuna damuwa kan yadda mayakan ISWAP suke barazanar mayar da hannun agogo baya kan nasarorin da aka samu.

A gefe guda kuma gwamnan har ila yau ya ce mika wuya da daruruwan mayakan Boko Haram suka yi a kwanan nan, ya sa ana samun zaman lafiya musamman a yankunan da ake ayyukan noma.

Gabanin jawabin na gwamna Zulum, Sanata Ndume ya fada cewa kwamitin ya kai ziyarar ne don nuna godiya ga gwamnatin jihar Borno kan yadda take ba sojoji hadin kai da taimako, batun da su ma dakarun kasar suka jaddada a baya.