HURIWA Ta Buƙaci A Kama Tsohon Alƙalin Alƙalai Na Najeriya

  • Ƙungiya Mai Kare Hakkin Bil’adama, HURIWA ta bayyana cewa ajiya aikin Alƙalin Alƙalai na Najeriya Tanko Muhammad bai isa ba, sai ta bukaci a Kama shi.

Tanko Muhammad ya ajiye aiki a matsayin Alƙalin Alƙalai na Najeriya na 17 a ranar Litinin ɗin nan.

Abinda ya sanya Tanko Muhammad ya sauka daga muƙamin sa ya biyo bayan zarge-zarge da akayi mashi ba karkatar da wasu kuɗaɗe daga Joji 14 na Kotun Ƙoli.

Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa Masu Shari’ar na Kotun Ƙoli a cikin wani ƙorafi da suka haɗa kai suka kai, sun zarge shi da rashin inganta jindaɗin su, da kuma cin zarafi a garesu.

Da farko HURIWA tayi ga Hukumar kula da ɓangaren Shari’a da Hukumar kula da Ɗa’a dasu yi bincike akan zarge-zargen da ake yi wa Tanko Muhammad.

A Jawabin da ta yi kan ajiye aikin, Ƙungiyar tayi kira da’a kama Tanko Muhammad daga Hukumar Kula da Hana Zagon Kasa.

A cikin sanarwar da Jami’in Hukumar ta fitar Kwamared Emmanuel Onwubiko tace ” Ajiye mukamin Tanko Muhammad a matsayin Alƙalin Alƙalai na Najeriya bai isa ba, EFFC, ICPC dole su tashi tsaye suyi bincike akan shi, idan gaskiya ne a kama shi tare da zartar masa da hukunci, kamar yadda manyan Alkalai guda huɗu suka zarge shi.

“Dole a zartar masa da hukunci kamar yadda wanda ya gada Walter Onnoghen aka gano shi akan zargin aka cire shi daga muƙami kamar yadda NJC da CCT suka yi.