Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta yi watsi da korafin da jamaiyyar APC reshen jihar Kano ta shigar

A cewar jamaiyyar Inec ta dauki ban gare na rashin baiyana sahihin sakamakon zabe na gaskiya, sai dai kuma ita hukumar ta Inec tace

jamaiyyar Apc bata da hurumin kalu balanta ko suka dan gane da sakamakon da baturen zabe Ahmed Doko ya ayyana cewa dan takarar jamaiyyar new Nigeian people party Abba Kabir Yusuf shine yayi na sara.

A cewar hukumar state din da doka ta basu dama suke da ikon sake zaben su sun hada da jihar Abia, Enugu, da kuma jihar Taraba itama ba a ko ina za ‘a sake zaben ba.

Haka zalika hukumar ta kara da cewa yunkurin Apc,n Kano na kokarin an sake zabe yaci karo da dokar hukumar sashe na 32/35/ 2022 da aka yiwa gyaran fuska

Daga karshe dai hukumar tace babu dalilin da zai sa ta ayyana zaben Kano a matsayin wanda bai kammmala ba wato (Inconclusive).