HOTUNA: Yan baranda sun kona Motoci, tare da tare hanya yayin yakin neman zaben Kwankwaso a Kano
Wasu ‘yan baranda da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a kan hanyar Na’ibawa zuwa Zariya a Kano.
Wasu ‘yan baranda da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a kan hanyar Na’ibawa zuwa Zariya a Kano.
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa magoya bayan na kan hanyar zuwa Kwanar Dangora ne da ke wajen birnin domin tarbar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Alhamis inda aka kai musu hari.
Kwankwaso na kan hanyarsa ta zuwa Kano ne domin gudanar da babban taron yakin neman zabensa na shugaban kasa.
Akalla motoci 10 ya zuwa yanzu an kai hari yayin da aka kona wasu da dama.
Harin dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da jam’iyyun da ke shiga zaben da ‘yan takararsu suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta biyu a Abuja.
Wani ganau da ya tsallake rijiya da baya, Tasiu Lawal, ya ce ya bi ta jikin motar da yake ciki.
“Na tsere da kyar. Alhamdulillah. Sai aka ce mana su (’yan baranda) suna nan suna jiranmu, don haka, muka tsaya Na’ibawa muka tabbatar muna da yawa kafin mu ci gaba.
“Ba tare da sani ba, sun zo ta kowane bangare suka far mana. Sun fara kai mana hari har da mata da adduna,” inji shi.
Jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, an tura su wurin da lamarin ya faru.