Gwamnoni zasu gana da Buhari kan tsadar rayuwa
Sanarwar ta bayyana cewa: “Wannan ne taro na farko da za’a yi kai tsaye tun bayan barkewar cutar ta Covid-19….
A bisa fargabar tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ke ciki, Gwamnoni 36 za su hadu a ranar nan Laraba 17 ga watan Agusta, 2022 a dakin taro na Banquet Hall na fadar shugaban kasa da ke Abuja, domin tattauna hanyoyin da za a bi.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Abdulrazaque Bello-Barkindo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa yanayin tattalin arzikin kasa za’a fi tattaunawa a yayin taron.
A cewar sanarwar, “Gwamnoni da dama sun yi tunanin cewa lokaci ya yi da za a gaya wa juna gaskiya ta hanyar fuskantar juna kan lamarin, gami da yin tunani a kai.
Sanarwar ta bayyana cewa: “Wannan ne taro na farko da za’a yi kai tsaye tun bayan barkewar cutar ta Covid-19.
Jaridar GANI YA KORI JI ta bayyana cewa.Abubuwa biyu za su yi fice a tattaunawar: tattalin arziki da tsaro. Wannan dai shi ne karon farko a cikin wannan shekara, sabanin rahotannin kafafen yada labarai na cewa Gwamnonin sun bai wa shugaban kasa shawara a baki daya game da zaftare ma’aikatan gwamnatin tarayya ‘yan shekara hamsin da sauran wasu munanan shawarwari da ake son a kara wa jama’a kunci, gwamnonin. za su yi taro tare domin yin la’akari da yadda za a yi wa tattalin arzikin kasar garambawul.
“Taron wanda, bisa ga gayyatar da Darakta Janar na kungiyar gwamnonin Najeriya, Mista Asishana Bayo Okauru, ya bayar, zai fara ne da karfe 2 na rana.