Gwamnatin Tarayya ta nemi a janye wasu tuhume-tuhume akan Emefiele
Gwamnatin tarayya ta bukaci a janye batun mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da ta shigar a gaban kotun tarayya da ke Legas a kan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da aka dakatar.
A ranar 25 ga watan Yuli ne alkalin kotun ya bayar da belin Emefiele a kan kudi naira miliyan 20 a kan tuhume-tuhume biyu na mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba, sannan ya bayar da umarnin tsare shi a gidan yari na Ikoyi har sai an cika sharuddan belinsa.
Sai dai hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake kama shi bayan wata arangama da jami’an gidan yari.
A ranar Talata, Daraktan shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta tarayya, DPP Mohammed Bakodo Abubakar, ya shaida wa mai shari’a Nicholas Oweibo cewa sabon takardar ya biyo bayan sakamakon ci gaba da bincike.
Sai dai lauyan da ke kariya, Joseph Daudu (SAN), ya nuna adawa da shi, yana mai cewa saboda gwamnati ta bijire wa umarnin kotu na bayar da belin Emefiele, ba za a iya karbar bukatar ta ba.
Da yake magana da manema labarai bayan zaman na ranar, Abubakar ya ce an shigar da sabbin tuhume-tuhumen a babbar kotun birnin tarayya (FCT).
Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya zargi Emefiele da “ba da fa’ida ba bisa ka’ida ba”.
A ranar 9 ga watan Yuni, Tinubu ya dakatar da Emefiele tare da bayar da umarnin gudanar da bincike kan wasu zarge-zargen da ake yi masa.
Daga baya Tinubu ya nada wani mai bincike na musamman da zai binciki CBN. A cikin wannan binciken, babban bankin ya fitar da bayanan kudi da aka tantance, wanda ya nuna cewa yana bin JP Morgan da Goldman Sachs kudaden da suka kai dala biliyan 7.5 a shekarar hada-hadar kudi ta karshen Disamba 2022.