Gwamnatin Tarayya ta fara duba akan Gyaran albashi

Hukumar karbar albashi da ma’aikata ta kasa ta ce ta fara aikin duba mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

Shugaban hulda da jama’a na NSIWC, Mista Emmanuel Njoku, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja.

Njoku ya ce a cikin tsarin duba mafi karancin albashin da za a yi a shekarar 2024, hukumar ta gudanar da tarurruka da horaswa kan yadda za a sa ido kan dokar mafi karancin albashi na shekarar 2019 a fadin kasar.

Ya ce dokar sa ido da za a fara a ranar 23 ga watan Janairu, zai taimaka wajen tabbatar da matakin bin ma’aikata da kungiyoyi na gwamnati da masu zaman kansu.

A cewarsa, tawagar da ke sa ido a tsakanin sauran abubuwa za su yi tambaya idan masu daukar ma’aikata suna kiyaye isassun bayanan albashi da yanayin hidimar ma’aikata.

“Aikin zai fadakar da jama’a da ma’aikata da kungiyoyi masu zaman kansu kan fa’idar tattalin arziki wajen bin biyan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

“Hakanan zai taimaka wajen samun bayanan asali kan manufofin biyan albashi da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu domin a wadata bankin bayanan hukumar kan biyan diyya ga ma’aikata.

“Tsarin sa ido zai shafi jihohi 36 na tarayya ciki har da babban birnin tarayya,” in ji shi.

Njoku ya ce tawagar da za ta sa ido kan atisayen za ta fito ne daga manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, da ma’aikatar kudi da tsare-tsare ta kasa.

Sauran masu ruwa da tsaki a cewarsa sun hada da shugaban ma’aikatan tarayya, ofishin akanta-janar na tarayya, ofishin kasafin kudi na tarayya da kuma hukumar kididdiga ta kasa.

Kakakin ya yi kira ga ma’aikatun gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, ma’aikatu da hukumomi da suka hada da kamfanoni mallakar gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago da su baiwa jami’an sa ido hadin kai.