Gwamnatin Nijar za ta yi bincike kan zanga-zangar ƙin jinin Faransa
Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun ce za su gudanar da bincike don tantance haƙiƙanin abin da ya faru cikin ƙarshen mako a garin Tera na jihar Tillabery bayan wata zanga-zangar ƙin jinin Faransa ta yi sanadin kashe wasu matasa.
Masharhanta a ƙasar dai sun ce abin da ke faruwa yana da ban takaici don kuwa zai karkatar da hankulan jami’an tsaro daga yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi, waɗanda su ne manyan abokan gaban Nijar.
Ƙungiyoyin fararen hula dai na ci gaba da kiraye-kirayen a gudanar da zanga-zangar ƙin jinin Faransa, yayin da rahotanni ke ambato Shugaba Mohamed Bazoum na cewa raba tsakanin Nijar da Faransa a wannan mawuyacin lokaci, ba shi ba ne mafita.