Gwamnatin Najeriya na barazanar saka dokar ta-ɓaci a jihar Anambra

PresidencyCopyright: Presidency

Gwamnatin tarayar Najeriya ta nuna alamun cewa mai yuwuwa ta sanya dokar ta-ɓaci a jihar Anambra d ke kudu maso gabashin ƙasar idan aka ci gaba da kashe-kashen da ake yi a jihar.

Gwamnatin ta sanar da haka ne ranar Laraba, da cewa za ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da an yi zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

Babban lauyan gwamnatin tarayyar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shi ne ya bayyana alamun haka a lokacin da yake jawabi ga ƴan jarida a ƙarshen taron Majalisar zartarwa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar, da ke Abuja.

Ya ce za su iya ɗaukar kowane mataki ciki har da sanya dokar ta-ɓaci a ƙoƙarinsu na tabbatar da an yi zaɓen cikin kwanciyar hankali ba kuma tare da wata matsala ba.

Ministan ya ce, idan tsaron ƙasar na cikin barazana, ana kai masa hari sannan dumokuraɗiyyar ƙasar da tsarin mulki ya tabbatar na fuskantar barazana, to ba wani mataki da za a kawar da yuwuwar ɗauka.

Ya ƙara da cewa a matsayinsu na gwamnati alhaki ya rataya a wuyansu na su tabbatar da ɗorewar tsarin dumokuraɗiyya kuma su tabbatar da tsaro ga lafiya da dukiya.