Gwamnatin Kano zata cigaba da karɓar harajin yan adaidaita sahu kullum

Gwamnatin jihar Kano ta ce za’a dawo da ƙarɓar Harajin kullum-kullum na matuƙa Baburan Adaidaita Sahu a faɗin jihar nan.
Lokacin da yake ganawa da Ƙungiyoyin sufurin Adaidaita Sahu na jihar nan, kwamishinan ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta ci gaba da karbar harajin ga matuƙa Adaidai Sahu domin ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba.
Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol ne ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a a helkwatartar Hukumar KAROTA.
Kwamishinan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za’a sabunta rijistar Adaidaita Sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu a faɗin jihar Kano.
Ya ce za’a ɓullo da sabbin tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin kullum-kullum tare da sabunta rijistar ba tare da an musguna musu ba, duba da yanayin da ake ciki na matsayin rayuwa.
Ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa Adaidai Sahun duba da yanayin da ake ciki. A don haka ko wanne matuƙi dole ne sai ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar nan baki daya.