Gwamnatin Kano ta Kori CMD 3, Ta Dakatar Da Likitoci da Ma’aikatan Jiyya
Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta amince da korar manyan jami’an kiwon lafiya na babban asibitin Imam Wali, Abubakar Imam Urology Center da Nuhu Bamalli Maternity Hospital tare da maye gurbinsu da gaggawa.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa sakataren zartarwa na hukumar Dakta Mansur Nagoda ya kuma amince da dakatar da duk wasu likitoci da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki na dare da rana a ranar Lahadi 30 ga Yuli, 2023.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Sulaiman ta fitar kuma ta bayyanawa manema labarai a daren ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an dauki matakin ne cikin gaggawa saboda sakaci da ma’aikatan da abin ya shafa ke yi wajen gudanar da ayyukansu ta hanyar kauracewa ayyukansu da barin marasa lafiya a hannun dalibai.
Sakataren zartarwa ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta amince da sakaci, da zuwa a makare ba, da gujewa aiki daga duk wani ma’aikacin lafiya, inda ya kara da cewa duk wanda aka samu yana so zai fuskanci takunkumi kamar yadda dokar ma’aikata ta tanada.
Ta yi kira ga sauran asibitocin da su kara hada kai domin za a sanya ido sosai kan dukkan kayayyakin aiki domin farfado da fannin lafiya a jihar.