Gwamnati Na Leƙen Asirin Wayoyin Ƴan Adawa, Ƴan Gwagwarmaya, Ƴan Jarida Da Wasu Ƴan Najeriya.

Gwamnatin jihohi da ta tarayya Najeriya su na amfani da kimiyyar leka sakwanni na sadarwar ‘yan Najeriya kamar yadda wani rahoto ya bayyana Rahoton ya nuna cewa hankalin gwamnatin ya fi karkata wurin bibiyar sakwannin ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida, ‘yan adawar siyasa da sauransu Hakan ya biyo bayan rashin tsaron da ya ke kara yawa a Najeriya don haka gwamnatin ta yanke wannan shawarar don leken asiri
Sabon rahoto ya nuna yadda gwamnati tarayya ta ke amfani da fasaha ta musamman don bibiyar sakwannin da ake tura wa mutum ko ya ke tura wa jama’a ta kafafen sadarwa, The Guardian ta ruwaito. Wani rahoto daga Action Group On Free Civic Space ya bayyana cewa gwamnati ta na amfani da fasahar ne wurin bibiyar ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida, ‘yan adawar siyasa da wasu kebantattun mutane.
Manufar rahoton shi ne kawo garanbawul a kan rashin tsaron da ya ke yunkurin raba kawunan jama’an kasa don haka gwamnatin ta sa ido akan ‘yan ta’adda.
NCC ta datse kafofin sadarwa a wasu jihohin arewa Ma’aikatar sadarwa ta kasa a watan Yunin 2021 ta datse duk wasu kafafen sadarwa a wasu jihohin arewa, Zamfara, Katsina, Yobe da Kaduna sakamakon yadda ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda su ka addabi yankin, inda su ka cutar da miliyoyin mutane har fiye da mutane 20,000 su ka rasa rayukansu.