Gwamna Zulum ya nemi afuwar iyalan Faston da aka harbe a Maiduguri
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ziyarci gidan Fasto Bitrus Tumba wanda ya mutu a lokacin wani rikici da ya kaure tsakanin jami’an hukumar tsara birane t jihar, BOGIS da wasu Kiristocin da ke bauta a cocin EYN da ke birnin Maiduguri.
Zulum ya nemi afuwar iyalan marigayin tare da jaddada cewa ana bincike yadda lamarin ya auku kuma za su yi kokarin wajen ganin sun yi adalci.
Gwamnan ya ce kowanne ɗan Borno na da ƴanci domin haka ba za su lamunci tauye hakki ko cin zarafi kowanne mutum ba.
Matakan da gwamnati ta dauka na rusa wasu gine-gine da ake ganin ba bisa tsari suke ba ya haifar da kazamin rikici da tayar da hankula a wasu yankunan Maiduguri.
Iyalan marigayin sun nuna godiyarsu da kulawar da suka samu daga Gwamna Zulum da cewa haka Ubangiji ya tsara.