Gwamna Zulum ya bai wa sojojin da aka raunata a Rann kyautar miliyoyi

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya ziyarci sojojin da aka jikkata a fafatawar da suka yi da mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a garin Rann na jihar.
Da yake tattaunawa da su ranar Litinin da dare a Asibitin Maimalari Barracks, gwamnan ya bayar da umarnin ba su kyautar naira miliyan biyar, inda za a ba su da kuma sauran waɗanda ke kwance a asibitin ko da kuwa ba su da alaƙa da fafatawar ta Rann.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta ce Kwamandan Bataliya ta 7, Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, ne ya tarɓi Gwamna Zulum.
A ranar Juma’a da ta gabata ne mayaƙan ƙungiyar ISWAP ko kuma Boko Haram suka kai wa sansanin sojan Najeriya hari a garin Rann na Ƙaramar Hukumar Kala Balge da ke kan iyakar ƙasar da Kamaru.

Wata sanarwa da rundunar sojan ta fitar ta ce dakarunta sun kashe gomman ‘yan bindigar tare da ƙwace makamansu. Sai dai soja bakwai sun rasu a gumurzun.