Gwamna Ortom ya sanya hannu ya dokar hana kiwo a fili ta 2017
Benue – Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya rattaba hannu a kan dokar hana kiwo a fili na 2017.
Majalisar dokokin jihar ta zartar da kudurin dokar ne a ranar Talata, bayan duban sashi da sashi na nazarin rahoton zaunannen kwamitin kan noma da albarkatun kasa na majalisar yayin zaman majalisar. Tun da farko Ortom ya nemi a sake bitar ne bisa dalilin cewa babbar dokar tana da wasu gyararraki da ke bukatar bita ta yadda za a dakile masu rashin mutunta dokar.
An ruwaito cewa, a yanzu dokar da aka yi wa kwaskwarimar ta nuna cewa duk wanda aka samu yana safarar dabbobi da kafa a cikin birane ko yankunan karkara ko kuma wani bangare na jihar zai biya Naira 500,000 a matsayin tara ga wanda ya yi laifi na farko.
Idan kuma aka kama mutum ya aikata laifin sau a karo na biyu zai biya N1 miliyan tare da sharuddan gidan yari da suka dace da zabin tara.
JARIDAR LEGIT.NG ta wallafa cewa Dokar da aka yi wa kwaskwarima ta kuma tanadi daurin shekaru 14 a gidan yari tare da zabin biyan tarar N5m ga duk wanda ya tura yaro mai karancin shekaru domin ya karya doka tare da cin tara a bangare saurana dabbobi kamar haka:
1. N50,000 kan kowace saniya
2. N10, 000 kan alade
3. N5,000 kan kowane akuya
4. N1,000 kowane nau’in tsuntsu ko kaji.