Gwamna Ganduje ya tafi Amurka yin kwas kan harkokin mulki

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tafi Amurka domin halartar wani kwas kan harkokin mulki. 

Wata sanarwa da Kwamashinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ya fitar ranar Talata ta ce kwas ɗin na mako ɗaya ne mai taken Authentic Leadership Development Programme wanda Sashen Kasuwanci na Jami’ar Harvard ya shirya.

Sanarwar ta ce gwamnan ya miƙa mulki ga mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna, wanda zai yi aiki a matsayin muƙaddashin gwamna. 

A watan Disamban 2020 ne aka ce jami’ar East Carolina ta bai wa Gwamna Ganduje muƙamin farfesa, sai dai jami’ar ta musanta batun tana mai cewa ba da yawunta wani ma’aikacinta ya ba shi muƙamin ba. 

An zaɓi Gwamna Ganduje a 2015 inda yanzu haka yake kan wa’adi na biyu a matsayin gwamnan Kano. Sai dai yana fuskantar rikicin siyasa a jam’iyyarsa ta APC tsakaninsa da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau.