Gobara Ta Tashi Babban Kasuwar Sokoto

Gobara Ta Tashi Babban Kasuwar Sokoto

Wani sashe na babbar kasuwar Sokoto da ake sayar da babura ya kone kurmus.

An gano cewa gobarar wacce ta faru da misalin karfe 6 na safiyar ranar Litinin, ta taso ne daga wani wurin juji.

Shugaban kungiyar masu sayar da babura Shehu Muhammad ya shaidawa wakilinmu cewa gobarar ta lalata babura da dama.

“Ba za mu iya kididdige adadin baburan da gobarar ta kone ba a yanzu saboda wutar na ci gaba da ruruwa.

Sai dai mutane da dama sun rasa shagunansu tare da babura saboda ba za su iya zuwa cikin lokaci ba saboda gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar yau.

“Mutanen hukumar kashe gobara ta tarayya da na jiha suna fafatawa don kashe ta amma na san za a dauki lokaci kafin su kashe su duka,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo agaji ga wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu a lokacin gobarar.

Aminiya ta ruwaito cewa an ga tashin gobara a kasuwar. A shekarar 2021 shaguna da dama sun lalace a kasuwar sakamakon barkewar gobara da ake ci gaba da ginawa.