Gobara Ta Tashi A Sansanin ‘Yan gudun hijira Da Ke Borno

Gobara Ta Tashi A Sansanin ‘Yan gudun hijira Da Ke Borno

Akalla yara biyu ne rahotanni suka ce sun mutu bayan da aka kone daruruwan ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno.

An bayyana cewa gobarar ta tashi ne da karfe 11:15 na safe a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Allamdari da ke Maiduguri.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Saidu, ya ce tawagarsa tare da ‘yan kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar.

Ya ce yara biyu ne suka rasa rayukansu tare da kona daruruwan tantuna sakamakon gobarar.

“Mun rasa yara biyu sakamakon barkewar gobara kuma muna kokarin tallafawa ‘yan gudun hijirar yanzu,” in ji Dokta Barkindo.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ana kokarin kashe gobarar amma har yanzu ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba.