Fina-finan Nollywood Ne Ke Haddasa Kashe-kashen Da Ake Yi Don Tsafi A Najeriya – Lai Mohammed

Matsalar kashe-kashen da ake yi don yin tsafi ta yi kamari a ‘yan kwanakin nan a Najeriya musamman a kudancin kasar. 

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ya ce kashe-kashen da ake yawan yi don tsafin neman arziki, na da alaka da fina-finan da masana’antar fim ta Nollywood ke shiryawa.

Mohammed ya fadi hakan ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Litinin dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Segun Adeyemi.

Ministan ya ce ya baiwa hukumar tace finan-finai ta NFVCB a Najeriya umarnin da ta kara azama wajen tace fina-finai da ke dauke da kashe-kashe na tsafi da ake yi.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin tarayya za ta kaddamar da wani shiri don fadakar da jama’a kan yawaitar wannan matsala ta yin kisa don yi tsafe-tsafe da ke kara yawaita.

“Ma’aikatar wayar da kan al’uma ta NOA ta riga ta fara hada kai da malaman addini da shugabannin gargajiya da kungiyoyi masu zaman kansu, don a sauyawa mutane tunani, musamman matasa, wadanda suke fadawa kangin burin ganin sun yi kudi cikin gaggawa.” Lai Mohammed ya ce.

Sai dai kamar yadda rahotannin suka nuna a baya, masana’antar ta Nollywood ta sha musanta wannan ikirari da ake yi inda manyan jarumai irinsu Kanayo O. Kanayi sukan mayar da martani.

Matsalar yawan kashe-kashen da ake yi don yin tsafi ta yi kamari a ‘yan kwanakin nan a Najeriya musamman a kudancin kasar.