Fari na barazanar yunwa ga dubban mutane : Somaliya
Akalla mutum daya cikin hudu na fuskantar barazanar yunwa a Somaliya a sabili da fari da kasar ke fuskanta a cewar Majalisar Dinkin Duniya a wani rahoton gargadi da ta fidda a yau.
Wannan dai na zuwa ne bayan karancin ruwan saman da kasar da ke fama da rikicin ta’addanci ta fuskanta na kusan damina hudu a jere. A cewar rahoton matsalar za ta yi kamarin da za ta kai ga barin kusan mutum miliyan 5 ga bukatar agajin gagawa na abinci.
Sama da shekaru 30 Somaliyar bata taba fuskantar irin wannan hali na fari da ta shiga ba. A cewar jami’in hukumar tallafin abinci Adam Abdelmoula, kananan yara daga shekaru biyar zuwa kasa wajen dubu 300 ke cikin hadarin fuskantar karancin abinci mai gina jiki cikin watanni masu gabatowa..
A watan da ya gabata ne mahukunta a Somaliya suka ayyana wannan matsala ta fari a matsayin agaji na gagawa.