FAGEN MARUBUTA A SIYASA

Author: Ahmad Habib Ibrahim

Bayan ficewar Tsohon shugaban jam’iyar PDP reshen jihar Kano wato Rabi’u Sulaiman Bichi, anjiyo matasa na ta kiraye-kirayen Marubuci Mustapha Adamu Indabawa a matsayin wanda ya cancanci zama Sabon shugaban

An jiyo matara irin su Abdullahi Nasidi Warure inda ya bayyana a shafinsa kamar haka

Sabuwar PDP A Kano In Sha Allahu Karkashin Shugabancin Matashin Bakwankwashe Me Burin Girmamar Wanann Tsari Namu Na Kwankwasiyya Mustapha Adamu Indabawa.

FATANMU A SHUGABANCIN PEOPLE’S DEMOCRACY PARTY (PDP) KANO STATE……….

Babu Shakka mafiya yawanmu matasa a cikin wannan jam’iyya tamu ta PDP muna bukatar shugaba Matashi Jarumi Wanda yakasance babu dare Babu rana wannan harkar itace a gabansa. Wanda zai kawowa jam’iyyarmu Da Tsarinmu Na Kwankwasiyya Daraja Da Daukaka Mara Iyaka da cigaban da zamujima muna Alfahari dashi acikin wannan jam’iyyar tamu..

Mu matasane ‘Yan Gwagwarmaya Danhaka munabukatar Shugaban da zai jagirancemu yazama matashi Fiye da mu. Hon, Mustapha Adamu indabawa Munshaida mutumin kirkine mara girman Kai gashi Lokaci Mai tsayi tare muke wannan aikin babu dare babu rana, Muna fatan burinmu bazaici karo da bukatar Jagoranmuba. Danmu Masu Biyyayane ga dukkanin wani tsari da jagora kwankwaso ze kawo bazamutaba Zama masu bijirewaba akan komai muddin daga Kwankwaso yake.

Muna fatan Allah ya tabbatar mana da wannan tsari Sannan muna addu’ar idan Allah Ya Tabbatar yazama Alkhai akan Dukkanin wanda yakeson jam’iyyarmu Da Babbabn Jagoranmu
Muna fatan idan Allah Yabaka Wannan matsayi Zakayi Kokari wajen chanja tsarin Siyasar Jiharkano daga yadda take ayanzu.

Harkullum Muna Kara Addu’ar 
Allah Yayiwa RMK/ Shugaban Nigeria 2023
Allah Yayiwa Abba Gwamman Kano 2023
Hon. Mustapha Adamu indabawa Allah Ya yadda Ayimaka Chairman PDP Party Saboda Shugaba (S.A.W)🙏”

Hakika matasa da dama sun ta kiraye-kiraye game da takarar ta Mustapha Adamu Indabawa a shafukan su

JAWABIN MUSATAPHA ADAMU INDABAWA

Mun jiyo marubucin wato Mustapha Adamu Indabawa yana bayyana farin cikin sa da Jadda goyan bayan sa ga Jagoran Kwankwsiyya wato Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taken jawabin sa ne da kalmar BAMU FARA DAN MU DAINA BA

Mai girma jagoran Kwankwasiya

“ABU KAMAR WASA KARAMAR MAGANA TA ZAMA BABBA

– Alhaji Garba Super

Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, ina mika godiya ga Alllah (SAW) Mai komai Mai kowa, wanda ba’a haife Shi ba kuma Bai haifa ba. Allah da bashi da shamaki tsakaninSa da bayinSa. Mai yadda Yaso a lokacin da Yaso kuma yadda Yaso, wanda kowa ke da bukata a wajenSa Shi kuma Baya bukatar komai a wajen kowa. Isasshe, Wadatacce, Gamsasshe, Mara farko balle Ya samu karshe. Dubun salati da salama ga fiyayyen halitta Muhammad Dan Abdullahi (SAW).

Maganar kujerar shugabancin PDP a Kano matasa sun dage suna bukatar canji saboda sun gaji da wasu mutane da suke labewa a jikin jagoran mu abin koyi Engr. Dr. Rabi’u Muaa Kwankwaso su sami abinda suka samu su watsar da matasa kuma daga baya su ci amana suyi butulci. Bayan wadannan matasa da su muke ta faman babatu a social media da sauran kafafen watsa labarai don yada wannan manufa amma a karshe sai a tafi a barmu cikin bacin rai da takaici har wani lokacin mu rasa abinda zamu rubuta saboda bacin rai amma dole sai mun kikiri abinda zamu rubuta don BAMU FARA DON MU DAINA BA. 

Yanzu na tabbatar da kalmar bahaushe da yake cewa “Yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba.” Komai mutum yayi duniya na kallonsa ko na sharri ko na alheri. Babu abinfa zan fadawa ‘yan uwana da abokan arziki sai godiya mara iyaka da fatan Allah Yayi musu sakayya da gidan aljanna. Wallahi bazan iya mantawa da kauna da mutunci da karama da irin yabon da ake yi mini a social media ba, kuma har yanzu ba’a daina ba don mu taken mu dama shine BAMU FARA DON MU DAINA BA, ko a safiyar nan da na tashi naga ana ta yabo na, Allah Ya saka da mafificin lada.

Ganin jajircewa ta da matsawa akan tafiyar Kwankwasiyya ya saka har yanzu banga wanda ya kalubalanci abinda wasu daga cikin matasa suka fara ba na neman canji a kaina. Wannan ya faru ne saboda duk wanda ya sanni akan akidar Kwankwasiyya ya sanni ban taba yin wani ra’ayi na daban ba a tafiyar siyasa sai ta Kwankwaso da Kwankwasiyya kuma bana da na sanin bin tsarin Kwankwaso kuma bazan daina bin wannan tsarin ba don mun aminta da cewa BAMU FARA DON MU DAINA BA.

Tun daga gwamnatin Shekarau ake yaudara ta da mukami da kudi ina kin karba. Wannan gwannatin kuwa ta aiko mini da sa don nayi layya na mayar mata da abinta. An yi yunkurin bani kudi naki karba, an yi mini tayin mukami duk naki karba. Wata daga cikin muhimman mata a wannan tafiyar ta gayyace ni zuwa Abuja don ganawa da SARKIN BACCI idan ina tsoron zuwa gidan gwamnati a Kano naki amincewa. Saboda wannan tafiyar ta Kwankwasiyya na rasa aiki a shekara uku da ta wuce amma gashi yanzu ina da aikin da yafi wancan don na yarda Kwankwaso na kan gaskiya kuma BAN FARA DON NA DAINA BA.

Akwai wadanda suka fara wannan yunkurin da mutane suke ta bugo mini waya suna ta fatan alheri wanda har zuwa yanzu babu wanda ya kira ni yayi mini magana mara dadi sai fatan Allah Ya bar zumunci kuma Ya bani ikon kulawa da su a duk halin da na sami kaina. Wannan kujera ba itace abu mafi muhimmanci ba a wajena. Abu mafi muhimmanci shine kauna da daraja da nake samu dalilin yunkurin da wadannan mutane suka yi kuma sun tabbatar da cewa BASU FARA DON SU DAINA BA.

A karshe nake son na mika godiya mara iyaka ga Fatima MuhammadLawan M Ahmad KarayeAhmad Ya’u GaroBuba UmarJiddah MusahKamila Muhammad SibaIbrahim Aliyu Yusip GamaNazir Adam SalihInuwa KwankwasoComr Muhammad HabeebRalliyyah Jibril Ado AyshaIsa Zanna IsaMubarak Muhammad, da sauran duk wanda ya taimaka wajen wannan tafiya da wadanda wasu dalilai basu basu dama ba da wadanda suje da niyar yin haka nan gaba da yawansu yakai bazai yiwu sai na iya rubuta sunan kowa ba saboda kada masu karatu su kasa karantawa.

BAMU FARA DON MU DAINA BA.”