EU ta nuna damuwa kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna su kai zuciya nesa a sabuwar takaddamar da ta barke tsakanin jami’an tsaron Isra’ila da kungiyar jihad al Islami ta Falasdinawa.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ce duk da yake Isra’ila na da hurumin kare kanta daga duk wata barazana, sai dai kuma duk wani matakin da ka iya illata rayuwar fararen hula abin gujewa ne, saboda haka dole ne bangarorin biyu da ke rikici su shafa wa zukatansu ruwan sanyi.
Wannan na zuwa a yayin da ma’aikatar tsaron Isar’ila ta ce a shirye take da ta cigaba da luguden wuta ba sani ba sabo a maboyar ‘yan kungiyar Islamic Jihad a zirin Gaza.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce sojojin kasar za su ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza har nan da mako guda, saboda hakan ba wata dama a yanzu ta hawa teburin sulhu don tsagaita wuta.
Jaridar VOA ta wallafa cewa Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta a wasu wuraren da ta kira maboyar ‘yan kungiyar Islamic Jihadi a zirin Gaza a ranar Jumma’a, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da wata karamar yarinya ‘yar shekaru biyar, baya ga raunata mutane 100, sai dai kungiyar ta Islamic Jihad harba daruruwan rokoki zuwa yankunan Isra’ila a wani mataki na martani.