Eriksen ya dawo kwallo

Dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen ya dawo tamaula, watanni bayan da ya samu bugun zuciya ana tsakiyar wasa.

Eriksen ya kife ana tsakiyar fafatawa tsakanin kasarsa da Finland a gasar cin kofin kasashen Turai ta EURO 2020.

A watan Janairu ne ya kulla yarjejeniya da kungiyar Brentford da ke gasar firimiyar Ingila, kuma a karon farko tun bayan da ya dawo jinya ya buga kwallo kusan awa daya.

Eriksen ya buga wasan sada zumunta da Brenford ta yi da Southend United, har ma ya taimaka aka ci kwallo a nasarar da kungiyar ta yi 3-2.

Yanzu haka dan wasan na kwallo ne da na’urar da ke taimaka ma zuciyarsa yin aiki.

Tun bayan da lalurar ta same shi ne Inter Milan ta raba gari dashi, la’akari da cewa doka bata yadda masu irin lalurarsa su buga gasar Serie A ba.

To amma babu irin wannan doka a gasar Firimiyar Ingila, wanda hakan ya bai wa tsohon dan wasan tsakiyar Tottenham din damar kulla yarjejeniya da Brenford.