EFCC ta kama tsohon shugaban hukumar raya Neja Delta da zargin sace biliyan 47

Jami’an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta kama tsohon babban darakta a Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Nsima Ekere, bisa zargin karkatar da naira biliyan 47. 

EFCC ta zargi Mista Ekere da kwashe kuɗin ne ta hannun ‘yan kwangila na ma’aikatar, kamar yadda mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwajaren, ya shaida wa Channels TV. 

Tsohon shugaban hukumar shi ne tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Akwa Ibom a jam’iyyar APC a zaɓen 2019. 

Nsima mai shekara 56 ya riƙe hukumar Neja Delta daga 2016 zuwa 2018.