Dokar sanya Hijab ga mata masu Labarai ta fara aiki a Afganistan

Mata masu gabatar da labarai a kafofin talabijin sun mutunta dokar gwamnatin Taliban da ta tilasta masu sanya nikabi. 

An ga matan sun rufe fuska yayin gabatar da labarai a kafofin talabijin na Afghanistan. 

A ranar Lahadi ne wa’adin da Taliban ta ba mata masu gabatar da labarai su fara rufe fuskokinsu don aiki da “hukuncin shari’a kan tufafin da ya dace da mata,” kamar yadda Taliban ta tilasta.

Shugabannin Taliban sun yi gargadin cewa duk ma’aikaciyar da ta bijerewa umarnin za a kore ta daga aiki.