Daurawa sun yi sulhu da Gwamna Yusuf, ya dawo a matsayin kwamandan Hisbah

Daurawa sun yi sulhu da Gwamna Yusuf, ya dawo a matsayin kwamandan Hisbah

– Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sun sasanta bayan barkewar rikici.

Daurawa ya tabbatar da sulhun a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook a daren ranar Litinin.Taron sulhun wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar Kano ya kasance a wurin gwamnan.

A ranar Talata ne kwamandan Hisbah zai koma kan kujerarsa.Rahotanni sun bayyana cewa, an aike da “Zauren Hadin Kan Malamai” — kungiyar manyan malaman addinin Islama zuwa Daurawa domin su kwantar da hankalinsa da kuma ba shi damar ci gaba da gudanar da aikinsa na shugabancin Hisbah.

Haka kuma gwamnati ta aike da shugaban majalisar dokokin jihar Kano Jibril Falgore da babban limamin masallacin kasa na Abuja Sheikh Ibrahim Maqari domin su gana da shi.

Idan za a iya tunawa Gwamna Yusuf ya soki dabarun “operation kau da badala” na hukumar, wanda ke neman yaki da lalata a jihar.Kasa da sa’o’i 24 da sukar gwamnan, Daurawa ya yi murabus, lamarin da ya janyo cece-kuce da suka da jama’a.

Ga dukkan alamu an kira taron ne a ranar Litinin din da ta gabata, saboda bacin ransa kan lamarin