Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC zai yi aiki da Wike : MASARI

Gwamnar Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa a sakamakon ganawar da Ahmad Bola Tinubu ya yi da Gwamnar jihar River Wato wike a kasar London sun samu matsaya akan Wike zai musu aiki don kaiwa ga gaci

Alhaji Ibrahim Masari wanda ya yi magana daga Landan, ya shaida wa BBC Hausa a ranar Laraba, cewa gaskiya ne Tinubu ya gana da Wike kuma za su ci gaba da ganawa a lokacin da ya dace.

A cewarsa,” taron ya kasance kan zaben shugaban kasa na 2023 kuma da yardar Allah za mu yi aiki tare da mai girma Gwamna Nyeson Wike, zai taimaka kuma za mu ci zabe cikin sauki, da yardar Allah.”

Da aka tambaye shi ko Wike na da niyyar komawa APC ne domin ya taimaka wa Tinubu ya ci zabe, Masari ya ce ba shi da ikon cewa Wike zai koma PDP, ya kara da cewa Wike ba sai ya bar PDP ba kafin ya taimaka wa kowa. yana so ya taimaka.