Dalilin Da Yasa Likitoci Ke Barin Najeriya – NMA
Kungiyar likitocin Najeriya NMA ta ce rashin albashi da kuma rashin ingantaccen yanayin aiki ya sa likitoci da ma’aikatan lafiya da dama barin Najeriya zuwa wasu kasashe don karin albashi.
Shugaban NMA na kasa, Dr Uche Ojinmah ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Alhamis yayin bikin bude taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na 2022 da aka gudanar a Gombe.
Ya ce likitoci a Najeriya suna fama da karancin albashi kuma ba su da kayan aiki da kuma yanayi mai kyau da za su yi aiki, don haka suka zabi barin kasar don nemawa kansu mafita, ci gaban da ke haifar da karancin ma’aikata a fannin kiwon lafiyar kasar kenan.
Dokta Ojinmah ya kuma yi Allah wadai da yadda gwamnatin Najeriya ke yi wa cibiyoyin kiwon lafiya wasarere ta karancin kudade, yana mai cewa har yanzu kasar ba ta aiwatar da sanarwar da aka a fitar a Abuja ta shekarar 2001 da ta ba da shawarar a ware kashi 15 na kasafin kudin ga bangaren lafiya.
“A shekara ta 2001, dukkan shugabannin kasashen Afirka sun hallara a Abuja inda suka yi taro kan yadda za a inganta fannin lafiya. Kuma a karshe sun yi sanarwar cewa kashi 15 cikin 100 na kasafin kowace kasa ya kamata a sadaukar da su wajen kula da lafiya.
“Abin takaici, tun wancan lokacin, Najeriya, kasar da ta karbi bakuncin taron ba za ta iya aiwatar da wannan sanarwar ba. Don haka, a bayyane yake cewa sun san abin da za su yi don inganta shi, amma watakila saboda dalilai na siyasa, ba haka ba ne, ”in ji shi.
Dokta Ojinmah ya bayyana cewa, domin inganta kididdigar kiwon lafiya a kasar nan, akwai bukatar gwamnati ta kara samar da kudade a fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da kayan aiki da isassun ma’aikata a dukkanin cibiyoyin lafiya a fadin kasar nan.
Ya kuma jaddada bukatar ma’aikatan kiwon lafiya su samu albashi mai kyau da kuma samar da yanayi mai kyau don gudanar da aikinsu.
Shugaban kungiyar ta NMA ya kara da cewa kungiyar ta damu matuka dangane da ayyukan ta’addanci a tsakanin likitocin, inda ya ce kungiyar na hada kai da daraktocin cibiyoyin kiwon lafiya domin kawar da harkar lafiya daga tashe-tashen hankula.