Dalilin Da Ya Sa Muke Sulhu Da ‘Yan Bindiga — Gwamnatin Sakkwato
Gwamnatin jihar Sakkwato ta fara yin sulhu da ‘yan bingida saboda rashin isassun jami’an tsaron da za su kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jiharKwamishinan Ayyuka da Al’amuran tsaro na jihar, Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ne ya bayyana haka ga manema labarai.Ya ce: “Mun yanke hukuncin yin sulhu saboda ba mu da isassun jami’an
tsaro da kayan aiki da za su kare kauyukanmu daga hare-haren ‘yan bindiga.“Gwamnatin Tarayya ce kadai za ta iya tallafa mana wajen samun aminci ta hanyar tabbatar da tsaro a jihar.“Mun gode wa Allah saboda ‘yan bindigar sun gaji da aikata laifuka, su ma suna son yin rayuwa kamar kowa, kuma sune wanda suka bukaci a yi sulhun,” a cewar Kwamishinan.Moyi ya bayyana cewa sulhun yana haifar da sakamako mai kyau, domin tunda aka fara yin sulhu ba a samu wani hari ko farmaki daga ‘yan bingida a jihar ba.Sannan ya roki gwamnatin tarayya da ta tallafawa jihar ta bangaren kayan aiki da kuma jami’an tsaro domin dakile matsalolin tsaro a jihar.Kwamishinan ya kara da cewa, jami’an tsaron Najeriya suna daga cikin wanda suka fi kowa iya aiki a duniya, sai dai suna bukatar kwarin gwiwa da kuma kayan aiki na zamani.