Dalibai sun ‘yantar da fursunoni shida a Suleja

Fursunonin shida na Cibiyar Kula da Tsaro ta Medium Security Centre Suleja sun sake samun ’yanci bayan wasu dalibai shida na Jewel Leading Light Academy da ke Abuja sun biya tarar su.

Dalibai shida – Dave Falade, Otse Unogwu, Ife Atilola, Zachary Abu, Ugomsinachi Okoronkwo da Nathan Oyinlola – duk a JSS 2, sun yanke shawarar taimakon agaji a karkashin shirin “Duke of Edinburgh Project”.

Daliban sun kai ziyara gidan yarin ne a ranar Talata inda suka biya kudi naira 120,000 a matsayin beli domin sakin fursunonin shida.

Haka kuma sun dauki kayan wanka masu yawa na sauran fursunonin da ke cibiyar.

Dangane da zaben fursunonin kuwa, daliban sun ce: “Mun ba da agajin kudi a tsabar kudi har Naira 120,000, tare da biyan tarar wasu fursunonin da suka nuna halin kirki da kuma sadaukar da kai ga gyarawa.”

Ɗaliban da ke tsakanin ’yan shekara 11 zuwa 12, sun ce: “Mun tsai da shawarar cewa a wannan aikin, za mu mai da hankali ne mu tara kuɗi da kayan aiki don tallafa wa ’yan’uwanmu da ke kurkuku.

“Yawancin lokuta, al’umma kan manta da kuma yin watsi da fursunoni. A matsayinmu na kungiya mun yanke shawarar cewa za mu sanya murmushi a fuskokin wadanda aka manta a cikin al’ummarmu.”

A cewarsu, sun tara tallafin kudi ta hanyar siyar da wasu kayayyaki a makaranta tare da kai ’yan uwa da abokan arziki domin tallafa musu.