Dakarun Faransa za su fice daga Timbuktu

Dakarun faransa sun fara shirin ficewa daga birnin Timbuktu dake kasar Mali, shekaru takwas bayan da Faransar ta fara shiga tsakanin a yankin Sahel mai fama da rikici.

Tun dai a watan Fabarairun shekarar 2013 ne dai shugaban Faransa na wancan lokacin Fancois Hollande ya kaddamar da fara ayyukan dakarun fiye da dubu biyar a yankin da nufin kawo karshen ayyukan masu tada kayar baya a yankin.

Yayin da dakarun Faransar ke shirin barin sansaninsu a Timbuktu, tuni dai aka fara dasa ayar tambaya kan makomar yankin yayin da ‘yan ta’adda ke kara zafafa kai hare-harensu a yankunan karkara.

Ana dai ganin nan da badi, adadin dakarun Faransa su ragu zuwa dubu uku a yankin na Sahel. Tun dai a shekarar 2013 masu tada kayar baya suka zafafa kai hare-hare a yankin, inda rikicin ya shafi kasashen Burkina da Nijar dake makaftaka da Malin.