Daga Jaridun Mu A Safiyar Yau

Barka da safiya!Ga takaitaccen bayani daga Jaridun Najeriya:

Taron yini biyu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago ya kawo karshe cikin rashin jituwa a ranar Talata, inda kungiyar kwadago ta Najeriya da shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa suka sha alwashin fara zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur a fadin kasar.

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta tanadi hukunci kan karar da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), ya shigar na kalubalantar nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Tinubu ne a matsayin wanda ya lashe zaben amma Obi ya ki amincewa da sakamakon ya garzaya kotun.

Wani jirgin sama a ranar Litinin da yamma, ya yi karo da wani gini a Ikeja, babban birnin jihar Legas. Jirgin ya fashe da wuta a kusa da filin jirgin saman Murtala Muhammed, MMIA. Jami’an bada agajin gaggawa na hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA sun ceto fasinjojin dake cikin jirgin.

Ma’aikatan Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) sun karbi babban ofishin hukumar a Abuja ranar Talata. Ma’aikatan da suke rike da alluna da kuma rera wakoki daban-daban, ma’aikatan sun bukaci a biya su albashin watanni bakwai.

Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP) Kayode Egbetokun a ranar Talata ya yi gargadi game da tashin hankali. Ya umarci kwamishinonin ‘yan sanda da su kara tsaurara matakan tsaro. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya ta sha alwashin fara zanga-zangar ta a fadin kasar ranar Laraba.

A ranar Talata ne tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai ya jefa majalisar dattawa a cikin rudani a lokacin da batun tantance shi a matsayin minista. Yayin da Sanatoci daga Jihar sa ta Kaduna suka nemi a ci gaba da yin hakan, cewa kasancewarsa tsohon Gwamna ne ya kamata ya gabatar da kansa sannan ya yi baka ya tafi, wasu Sanatocin kuma na ganin ya kamata a tambayi tsohon Gwamnan kan iya aikinsa na Minista. .

Umarnin zama a gida na mako biyu da Simon Ekpa ya bayar ya gamu da cikas. Mazauna jihohin Kudu maso Gabas sun yi watsi da wannan umarni tare da halartar jaddawalin su na yau da kullun a ranar Talata. A jihar Imo, masu kasuwanci a cikin babban birnin Owerri, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun bude wa kwastomomi. Bankuna, kasuwanni, manyan kantuna, gidajen cin abinci da masu sana’a sun yi aiki ba tare da wata matsala ba a duk fadin yankin.

Shugaban kasa, Bola Tinubu da jam’iyyar APC, a ranar Talata, sun dage cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, ba dan jam’iyyar ba, ba shi da hurumin kalubalantar sakamakon zaben. zaben 25 ga Fabrairu. Haka kuma sun bukaci PEPC da ta hana shi sake tsayawa takara idan har aka soke zaben.

Jam’iyyar PDP ta yi watsi da watsa shirye-shiryen da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Litinin a matsayin tarin alkawuran karya da masu rike da mukaminsa suka yi cikin gaggawa. Sakataren yada labarai na kasa, Debo Ologunagba, a wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, ya yi ikirarin cewa alkawuran na da nufin yi wa ’yan Najeriya zagon kasa da yaudarar ‘yan kwadago.

A ranar Talatar da ta gabata ne aka gurfanar da wasu mutane uku a hedikwatar ‘yan sandan jihar Osun kan harin da aka kai a wata Cocin Celestial da ke kauyen Odu kusa da Osogbo. Wadanda ake zargin sun kai hari cocin ne a lokacin da suke sintiri da sanyin safiyar Talata.