Daga Jaridun Mu A Safiyar Yau
Bayan shekara 15 ana tafka shari’a, kamfanin mai na Shell ya amince ya biya wasu manoma uku da kauyukansu da ke yankin Neja Delta diyyar Yuro miliyan 15 saboda gurbata musu muhalli.
Mahara da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace limanin cocin katolika na Jihar Benue, Rabaran Fada Mark Ojotu.
Gwamnatin jihar Osun tayi wani bincike, ta gano tsohon Gwamnan ta ya bar ofis da motocin N2.9bn a dalilin haka Ademola Adeleke ya bada umarnin a gaggauta dawo da duk motocin.
Kungiyoyi sun yi zanga-zangar a Hedikwatar CBN suna neman Emefiele yayi murabus kn dambarwar zargin sa da hannu a daukar nauyin ta’addanci.
Dan tarakar gwamnan Kano a Jam’iyyar PDP da kotu ta soke, Sadiq Aminu Wali ta ayyana Mohammed Abacha, ya ce zai daukaka kara.
Kotu ta dakatar da Ganduje daga gina shaguna a jikin Makarantar Sikandiren Kwakwachi.
’Yan sanda a Jihar Ogun sun cafke wani matashi bisa zargin kashe wani direban mota Obafunsho Ismail kan jayayya (musu).
Gwamnatin Nyesom Wike ta bada umarni a rufe wani ofishi da jam’iyyar PDP take kamfe a Ribas.
Wata kotun Majistare da ke Kano ta daure wani matashi da aka gurfanar bisa zargin sa da yunkurin satar kazar wani mutum.
Aminu Adamu, matashin nan da kotu ta tsare a gidan yari kwanakin baya kan tsokanar matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ya kammala jami’a.
Akalla dakarun soji 16 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota a Arewa maso Gabashin kasar Indiya.
Gwamnatin Habasha ta sha damarar yaki da kuraye da ke farwa mutane.
Gwamnatin Burkina Faso ta kori jami’ar Majalisar Dinkin Duniya daga kasar.
Manchester United sun hau teburin tattaunawa da PSV Eindhoven don ɗauko dan wasan gefe na Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 23.
Kocin Manchester United Erik yace burinsa Ƙungiyar ta buga wasan zakarun turai a badi.