Daga Jaridun Mu A Safiyar Yau

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, Ya Karbi Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan, a fadar Aso da ke Abuja, jiya Juma’a.
Atiku Abubakar zai zauna a gefe yana kallon rikicin da ya kaure tsakanin ‘Yan G5 da ba su goyon bayan takarar da yake yi a PDP.
Rundunar ’Yan Sandan babban birnin tarayya, ta cafke gungun wasu mutum 10 da ake zargin su da kai hare-hare a Abuja da Jihar Nasarawa.
Gobara ta kone wasu gine-gine a biyu da ke dauke da gidaje akalla 40 a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Gobir Kalgo Alhaji Haruna Jada, Jihar Kebbi.
Rundunar ‘yansandan Jihar Ribas ta ce ta kai samame a maboyar ‘yan kungiyar Biyafara (IPOB) da ke karamar hukumar Oyigbo a jihar.
Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 35 a gidan gyaran hali, kan laifin zamba cikin aminci a jihar Oyo.
Wata rugar Fulani da ta kafu sama da shekara 70 a Obudun jihr Cross Rivers tace tana so gwamnati ta gyara makarantun da suka lalace a wurin.
Duk da rahotanni na ta yawo cewa ‘Yan kungiyar G5 sun amince su goyi bayan Bola Tinubu a 2023, an fahimci ba a tsaida magana ba, domin Wike ya fice daga taron a fusace.
Hamshaƙan masu kuɗin duniya irinsu Elon Musk da Zuckerberg sun tafka muguwar asarar tirliyan $1.4 a 2022.
Za a rika yi wa matafiya daga China gwajin korona a Birtaniya
Rundunar sojin Kamaru tace an kashe Sojanta a wani harin kwanton bauna da ‘Yan jihadi suka kai.
Afrochella: Masu zuwa babban casun Ghana sun kaɗu jin cewa an daina shi.
Kotun Mali ta yanke wa sojojin Ivory Coast 46 hukuncin daurin shekaru 20.
Madrid ta ce ko Belligham ya fi €100m za ta saye shi.
Cristiano Ronaldo ya shiga kulob ɗin Al Nassr na ƙasar Saudiyya kan wata yarjejeniya da zai ba shi damar zama har shekara ta 2025.