Daga Jaridun Mu A Safiyar Yau
Barka da safiya! Ga takaitaccen bayani daga Jaridun Najeriya:
Wasu gungun manyan hafsoshin sojan kasar Gabon sun sanar da kwace mulki. Jami’an sun yi ikirarin cewa su ne wakilan dukkanin jami’an tsaro da na tsaron kasar Gabon, tare da tabbatar da ikonsu a kan al’ummar kasar.
Shugaba Bola Tinubu ya mayar da martani kan juyin mulkin da aka yi a Gabon na baya-bayan nan, inda aka yi wa shugaba Ali Bongo daurin talala. Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce fadar shugaban kasar na sa ido sosai tare da nuna matukar damuwa ga zaman lafiyar al’ummar kasar nan da kuma yadda ake ganin rigimar mulkin kama-karya da ke yaduwa a yankuna daban-daban na nahiyar.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun runduna ta 343 Artillery Regiment dake gudanar da aikin yaki da satar mai a ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023, sun fatattaki wani sansanin barayin mai da ke unguwar Obokofia a jihar Imo. Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta bayyana cewa, dakarun ‘yan banga sun kama buhu 15 da kuma Jerry gwangwani 13 na Automotive Gas Oil (AGO) da aka boye ba bisa ka’ida ba a sansanin.
Tsohon dan majalisa kuma fitaccen mai sukar al’umma, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa zabe mai guba ne ke haddasa rugujewar dimokuradiyya a Afirka. Kalaman Sani na zuwa ne a daidai lokacin da aka yi juyin mulki a kasar Gabon da ke tsakiyar Afirka.
An buga wani faifan bidiyo na hambararren shugaban Gabon, Ali Bongo yana kira ga “abokansa” da su yi magana bayan nasarar juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar mai arzikin man fetur a tsakiyar Afirka. Bongo a cikin faifan bidiyon ya nemi abokansa da su “yi hayaniya” game da mutanen da suka kama shi da iyalinsa.
Pa Taiwo Akinkunmi, wanda ya zana tutar Najeriya ya rasu. Dan sa, Akinkunmi Akinwumi Samuel ya tabbatar da rasuwarsa a shafin sa na Facebook.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ja kunnen shugabannin jam’iyyar sa ta PDP da su dakatar da shi ko kuma su ladabtar da shi. Wike ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin hirarsa da shirin Siyasar Yau na Channels Television.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayyana cewa jirgin kasan layin dogo da aka dade ana jira zai fara kasuwanci a wata mai zuwa, 4 ga watan Satumba. Sanarwar na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta na X, ranar Laraba.
Kwamitin wucin gadi da ke binciken rashin fitar da kudade cikin asusun kula da gidaje na kasa ya gayyaci kamfanonin inshora 54 a Najeriya da su gurfana a gabansa kan rashin fitar da naira biliyan 267 cikin asusun. Shugaban kwamitin, Dachung Bagos, a yayin wata tattaunawa da wakilan kamfanin inshorar AIICO, ya ce kamfanonin inshora sun gaza tura kudi zuwa NHF kamar yadda doka ta tanada.
Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya karyata zargin dakatar da Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023. Babban mai binciken jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Laraba a hedikwatar NNPP na kasa da ke Abuja.