Da dumi-dumi: Mai sukar Aisha Buhari, Aminu, zai gana da Buhari bayan an sallame shi

An saki mai sukar uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, Aminu Mohammed Adamu daga gidan yari ba tare da wani sharadi ba.
Aminu, dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, jihar Jigawa, ana sa ran zai gana da mijin Misis Buhari, shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin ya sake haduwa da iyalansa.
An kama shi ne da laifin yiwa uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari cin zarafi a shafin Twitter, kuma an gurfanar da shi a asirce a kotu tare da tsare shi a gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja.
LEADERSHIP ta rawaito cewa , Aminu yana Aso Villa a Abuja kuma yana jiran ganin Shugaba Buhari.