DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Wakilin NNPP Yerima
Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha da ke Kano ta soke zaben Muktar Umar Yerima na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Kotun ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Yerima tun da farko.
Mai shigar da kara, Hafizu Kawu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kalubalanci bayyanar Yerima, yana mai cewa bai cancanta ba.
DAILY POST ta Rawaito cewa INEC ta ayyana Yerima a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar wakilai na mazabar Tarauni.
Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin mutum uku na kotun karkashin mai shari’a I.P. Chima ya ce Yerima bai cancanta ba saboda ya yi jabun takardar shedar firamare.
Kotun dai ta ce kariyar da Yerima ya yi na cewa ya sauya suna a shekarar 2022 bai rike ruwa ba, kasancewar yana amfani da sunaye guda uku (Umar Mukhtar Zakari) a fasfo dinsa na kasa da kasa tun a shekarar 2009, yayin da takardar shaidar makarantar firamare ke dauke da Umar Mukhtar.
Har ila yau, makarantar firamare da aka ce, makarantar firamare ta Hausawa, ta yi watsi da takardar shaidar da korarren dan majalisar ya bayar.
Don haka aka ce jam’iyyar NNPP ba ta da dan takara a zaben.