Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS ta fitar da sanarwa a kan kama gwamna CBN Godwin Emefiele

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta karyata rahotannin da ke cewa jami’anta sun mamaye ofishin babban bankin Najeriya, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

An samu rahotannin cewa jami’an ‘yan sandan sirri sun mamaye babban bankin na CBN a ranar Litinin da ta gabata da nufin cafke gwamnan babban bankin.

Sai dai DSS a wata sanarwa da kakakinta, Peter Afunanya ya fitar, ya bayyana rahoton a matsayin na bogi da yaudara.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An jawo hankalin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan labarin karya da ake yadawa cewa jami’anta sun mamaye babban bankin Najeriya tare da kama gwamnansa, a yau 16/1/23.

“Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce.”