Cyril Ramaphosa ya mika wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar amsoshi kan zargin boye wasu kudade

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar amsoshi kan zargin boye wasu kudade da aka yi a wani gidan gonansa na alfarma.

Ofishin jami’an kare hakkin jama’a ya yi barazanar aika sammaci ga shugaban kasar a farkon wannan mako bayan cikar wa’adin bayar da bahasi.

A watan Junin da ya gabata ne dai, hukumar yaki da cin hancin ta bude bincike kan yiwuwar keta ka’idojin zartarwa bayan da aka zargi shugaban Afrika ta Kudun da bai wa barayi cin hanci, don rufe bakinsu game da badakalar barnar da ta auku a watan Fabrairu 2020 a gonarsa. Ana zargin an sace tsabar kudi dala miliyan 4.

Tuhumar ta haifar da matsin lamba akan shugaba Ramaphosa daura da rikicin da jam’iyyar ANC mai mulkin kasar ke ciki, wadda ta samo asali daga rahoton ‘yan sanda da tsohon shugaban leken asirin kasar Arthur Fraser ya shigar a watan jiya.