Cuter Kyandar biri ta bulla a Isra’ila

Isra’ila ta tabbatar da ɓullar kyandar biri da ke ci gaba da bazuwa a kasashen Turai.
Haka ma switzerland ta tabbatar da ɓullar cutar, inda yanzu yawan ƙasashen da cutar ta ɓulla suka kai 14.
Ƙasashen biyu sun ce sun gano mutanen da suka kamu, waɗanda suka yi balaguro, amma Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan wasu da take zargi.
Zuwa yanzu mutum 80 aka tabbatar da sun kamu da cutar a Turai da Amurka da Canada da Australia.
Cutar ta fi yawa a ƙasashen tsakiya da yammacin Afrika.