Cibiyar Horar da Mata 20 Aikin GSM A Kano

Cibiyar fasahar sadarwa da ci gaba (CITAD) ta fara horas da wasu zababbun mata guda 20 na tsawon mako uku a kan aikin GSM da gyaran wayar hannu a jihar Kano.

Horon wanda ya fara a ranar Asabar, ya samu matasa mata da ‘yan mata daga yankin Sani Mainagge da ke karamar hukumar Gwale a cikin babban birnin.

Babban Darakta na CITAD, Dakta Y Z Yau, ya ce sun gudanar da horon ne da nufin baiwa mata sana’o’in gyaran wayar hannu domin su zama masu dogaro da kai da kuma cike gibin da ake samu a fasahar zamani a tsakanin mata.

Yau wanda ya samu wakilcin Ahmad Abdullahi Yakasai ya ce Lenovo ya dauki nauyin wannan horaswar, inda ya bukaci mahalarta taron su mai da hankali su koyi sana’o’i.