CBN ta baiwa TajBank lasisin gudanar da harkoki a faɗin ƙasa
Babban Bankin Ƙasa, CBN ya baiwa bankin TajBank, wanda shi ne kan gaba wajen harkar bankin da ba kudin ruwa, lasisin gudanar da harkokin banki a ko ina a faɗin Nijeriya.
Manajan-Darakta na bankin, Hamid Joda ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a yau Laraba.
Joda ya ce bankin ya samu lasisin ne baya ga ɗumbin lambobin girma da ya samu a shekaru biyu da ya fara gudanar da harkokinsa domin yaba wa bisa irin gagarumar rawar da ya taka a harkar banki a Nijeriya.
A cewar Joda wannan wata ƙarin nasara ce a kan irin ƙwazon da ya ke na gudanar da harkar banki daidai da zamani.
Ya kuma godewa CBN da ya baiwa bankin lasisin fara gudanar da harkar banki a faɗin ƙasa, inda ya ce “hakan zai sa mu kara samun kwastomomi.”