Buhari ya zargi Amnesty da goyon-bayan IPOB

Shugabajn Najeriya Muhamamdu Buhari ya zargi ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty da goyon-baya ta’addanci da ake aikatawa a ƙasar.

Shugaban a wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakinsa Malam Garba Shehu ya ce Amnesty wacce doka ba ta bata damar gudanar da ayyukanta a Najeriya ba, a yanzu haka ta jefa siyasar cikin gida a lamuranta.

Shugaba Buhari ya zargi ofishin Amnesty na Najeriya da neman farantawa wasu tsiraru da kira ga ƙungiyar ta binciki ayyukan jami’anta a Abuja.

Sanarwar dai ta ce Amnesty na kamba wasu batutuwan tsaron cikin gida da kare jagoran ‘yan awaren IPOB wanda a dalilisan mutane da dama suka rasa rayukansu a Najeriya.

Sannan ya ce ana amfani da Amnesty wajen rufe manyan laifuka, kuma wannan yanayi ne na alla-wadai da ake gani a wata kasa ta Afirka.

Buhari ya bukaci ƙungiyar ta kaddamar da bincike kan jami’anta da ya zarga na yaɗa labaran boge, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yakar ‘yan ta’adda babu sassautawa. Kuma ba za su saurari batutuwan da Amnesty ke yaɗawa ba.