Buhari ya taya Bishop Okpaleke murnar nadinsa a matsayin Cardinal na Paparoma
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bayyana farin cikinsa da nadin Bishop Peter Okpaleke na Diocese Ekwulobia, jihar Anambra, a matsayin Cardinal a Cocin Katolika da Fafaroma Francis ya yi.
A wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yammacin Laraba ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Garba Shehu, Buhari ya yabawa Paparoma bisa yadda ya samu dan Najeriya mai nagarta a matsayin Bishop Okpaleke a matsayin daya daga cikin mutane biyu da aka zaba daga nahiyar Afirka.
Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari ya yi maraba da nadin Bishop Okpaleke a matsayin Cardinal na 4 daga Najeriya.’
A cewar Shehu, Shugaba Buhari ya kuma taya kungiyar Kiristocin Najeriya murna kan wannan zabin, inda ya bayyana Cardinal din da aka nada a matsayin wanda ya cancanta, kuma samunsa a wannan matsayi zai amfani kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Shugaban ya kuma yaba da jajircewar cocin Katolika na tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban kasar Najeriya. Ya kuma bayyana kokarin Cocin na yakar cutar ta COVID-19 da kuma goyon bayanta da jajircewarta na tallafawa talakawa da mafiya rauni a cikin al’umma.”